Ci gaban rikicin Somalia | Labarai | DW | 15.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban rikicin Somalia

A ƙalla mutane 8 su ka rasa rayuka a ƙasar Somalia, a cikin wasu tagwayen hare-hare, da su ka rusta da birnin Mogadiscio.

Hare-haren sun yi setin mataimakin magajin garin Mogadiscio Osman Dagatur, wanda ya ƙetara rijiya da baya.

Gwamnati ta rataya alhakin wannan hari, ga dakarun kotunan Islama.

Tun bayan korar kotunan Islama,daga karagar mulkin Mogadiscio, babban birnin na Somalia, ke fama da tashe-tashen hankulla.

Masu tsatsauran ra´ayin addinin Islama, sun sha alwashin ɗaukar fansa, da kuma cilastawa sojojin Ethiopia, da su ka kawo tallafi ga gwamnati, su fice daga ƙasar Somalia.