1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban rikicin Afghanistan

April 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuMm

A ci gaba da tashe-tashen hankulla a ƙasar Afghanistan, a ƙalla mutane 20 su ka rasa rayuka, yau laraba, a hare-hare daban daban, da mayaƙan Taliban su ka ƙaddamar.

Mutanen da su ka mutun, sun haɗa da sojoji 6, masu biyyaya ga gwamnati.

Kazalika, rundunar Taliban, ta yi assara sojojin ta 5, a cikin wannan ba ta kashi.

Gwamnatin Afghanistan, tare da haɗin gwiwar dakarun rundunar ƙungiyar tsaro ta NATO, sun sha alwashin kakkaɓe, Aghanistan daga barazanar yan taliban , to saidai ya zuwa yanzu, wankin hulla na shirin kai su dare, ta la´akari da turjiyar ba zata, da yan taliban su ka nuna.

Gobe idan Allah ya kai mu,ministocin harakokin waje, na ƙasashe membobin ƙungiyar tsaro ta NATO, za su shirya zaman taro a birnin Oslo na ƙasar Nowe.

Rikicin Afghanistan na daga cikin ajendar batutuwan da za su tantana akai.