Ci gaban rikicin ƙasar France | Labarai | DW | 25.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban rikicin ƙasar France

An waste baran baran, yammancin jiya,tsakanin Praministan France, Dominique de Villepin,da tawagar ƙungiyoyin ƙwadago, a ganawar da su ka yi fadar Matignon, dake birnin Paris.

Tawagogin 2, sun tantana a game da matasalar CPE, wato Contrat Premiere Embauche , dokar nan ,da a halin yanzu, ake ci gaba da kai ruwa rana, kanta a ƙasar France.

ƙungiyoyin ɗallibai, da na ƙwadago sunyi watsi da wannan sabuwar doka, da gwamnati ta ƙirƙiro, ta fannin ɗaukar sabin ma´aikata.

A sakamakon ganawar ta jiya, Dominique de Villepin da yan ƙwadago, sun yi tsawuwar gwamen jaki, a akan manufofin su.

Shima shugaban ƙasa Jaques Chirac, ya nuna goyan baya ga Pramisnita, ta hanyar bada odar aiwata da dokar.

A tsawan satin 2, da su ka gabata, ɗallibai a makarantu da jami´o´I daban-daban na France, sun gudabar da zanga zanga, domin cilastawa gwamnati ta lashe amen ta.

Sun kuma sha niyar ci gaba, da gwagwarmaya har sai sun cimma nasara.

Ranar talata mai zuwa, sun ƙara kiran magoya bayan su, zuwa wata gagaramar zanga zanga.