Ci gaban rikici a Timor ta gabas | Labarai | DW | 30.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban rikici a Timor ta gabas

A na cigaba da tashe tashe hankulla a Dili, babban birnin Timo ta gabas.

Da sanhin sahiyar yau, matasa masu adawa da juna, sun ƙara gwabzawa, gap ga fadar shugaban ƙasa.

Kazalika, sun kai samame, ga shaguna, tare da ƙona gidaje da motoci.

Rahotani daga birnin, sun ambata cewar, dakarun ƙasar Austrayila, da su ka kai ɗauki, da gwammnati na ci gaba da tarwatsa wannan matasa, da ke shirin tada zaune tsaye a ƙasar.

Tun ranar jiya, shugaban ƙasa Xanana Gusmao, da Praminista Mari Alkatiri, ke gudanar da zaman taro, da zumar lalubo hanyoyin kuɓuta, daga wannan rikici.