Ci gaban rikici a ƙasar Burma | Labarai | DW | 14.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban rikici a ƙasar Burma

Gwamnatin,mulkin soja a kasar Burma ko Myanmar, na ci gaba da yin kame-kamen kann mai uwa da wabi, ga masu zanga-zanga.

Idan dai a na tune, a watan da ya gabata zangar ta munana , inda jami´an tsaro su ka yi anfani da ƙarfin bindiga, domin murƙushe wannan tashe-tashen hankulla.

Mutane da dama sun rasa rayuka, a sakamakon ɗaukar wannan mataki,wanda ya sha samin suka daga ƙasashen ƙetare.

Sannan gwamnatin ta capke dubunan jama´a, wanda har yanzu ke cikin kurkuku.

A jiya asabar, masu zanga-zangar sun ce sai dai a kashe tsofuwa kann daddawar ta, a game da haka, su ka sake fitowa a titina don nuna fushi, ga yadda sojoji ke gudanar da harakokin mulki a ƙasar.

Wannan sabuwar zanga-zanga na wakana, a yayin da wakilin mussamanan na MDD a kasar Mayanmar ,Ibrahim Gambari, ya shiga wani saban ranagdi ,ayankin Asia,da zumar samo bakin zaren warware rikicin ƙasar Burma.

A ranar alhamis da ta wuce, komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, ya bayana sanarwar yin Allah wadai, ga matakin da gwamnatin ta ɗauka, a kan masu zanga-zangar.