1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban kone konen motoci da gidaje a kasar Fransa

November 7, 2005
https://p.dw.com/p/BvMC

A karro na farko bayan kwanaki 11 na zanga zanga ,da kone konen motoci shugaban kasar Fransa Jak Shirak ,ya gabatar da jawabi, jim kadan bayan da ya kammala taron gaggawa tare da hukumar tsaro ta kasa.

Shirak, ya bayana matukar damuwa a game da wannan kone kone da ya shafi motoci da gidaje da ma wasu wuraren ibada da shuguna.

Daga farkon rikicin ranar 27 ga watan oktober ya zuwa yanzu, motoci kussan 3.500 su ka wuta.

Kone kone ya fara bazuwa cikin birane, inda daga daren asabar zuwa sahiyar lahadin jiya, a Paris babban birnin kasar a ka kona motoci 32.

Duk da matakan tsaro da gwamanti ta dauka an cigaba da zanga zangar, inda a daren lahadi zuwa sahiyar litinin a ka kona motoci kussan 900.

A halin da a ke ciki jami´an tsaro na ci gaba da sintiri tare da kame kamen mutanen da ake tuhuma da hannu a cikin wannan ta´adi.

Shugaban kasar ya tabbatar da za su gurfana gaban kotu domin hukunta su daidai da dokokin kasa.