Ci gaban harkokin siyasa a Pakistan | Labarai | DW | 03.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban harkokin siyasa a Pakistan

A wannan makon ne aka shirya isar tawagar Jami´an binciken Biritaniya, izuwa ƙasar Pakistan. Tawagar za ta taimaka ne, wajen laluben mutanen dake da hannu, a kisan gillar da akayiwa Benazir Bhutto. Matakin a cewar rahotanni, ya biyo bayan kiraye- kirayen hakan ne daga ɓangaren ´yan adawa ne na ƙasar. Tuni dai Pakistan ta bayyana amincewarta da wannan mataki. Rahotanni sun nunar da cewa kisan da akayiwa Bhutto, a yanzu haka ya haifar da ɗage zaɓen gama gari da aka shirya gudanarwa a ƙasar, a ranar 8 ga watannan. Hukumar zaɓen ƙasar ta ce a yanzu an shirya zaɓen ne, a ranar 18 ga watan Fabarairun wannan shekara. Jam´iyyun adawa sun bayyana ɓacin ransu a game da wannan mataki, da acewa Gwamnati za ta yi amfani da damar wajen shirya maguɗi.