Ci gaban hare-hare a Somalia | Labarai | DW | 15.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban hare-hare a Somalia

Wasu mutane ɗauke da manyan makamai, sun kai hari ga cibiyar hukumar Kiwon lahia, ta Majalisar Ɗinkin Dunia, dake birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia.

Gwamnatin ƙasar ta zargi dakarun kotunan da wannan aika-aika.

Sakataran zartaswa na ƙungiyar tarayya Afrika, Alfa Umar Konare, yayi Allah wadai, da wannan hari.

Sannan ya ce, ya zama wajibi, sojojin ƙasar Ethiopia, su ci gaba da kai tallafi ga ƙasar Somalia.

Alfa Konare, ya jaddada kira ga ƙasashen Afrika, su gaggauta aika sojoji a Somalia.

Ya zuwa yanzu dakarun ƙasar Uganda, kafai su kimanin 1.500 ke ci gaba da sintiri a birnin.

Baki ɗaya ƙungiyar taraya Afrika, ta bukaci aika dakaru dubu 8, a wannan ƙasa domin kwantar da tarzoma.