1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban hare hare a Iraqi

Hare haren bam guda 3 sun kashe akalla mutane 24a garin Kirkuk dake arewacin Iraqi.

Rahotanni daga majiyoyin yan sanda da na asibiti sunce,daya daga cikin bam din ya fashe ne a kusa da wani shingen yan sanda,daya bam din ya sake fashewa yayinda jamaa suka taru suna duba barna da bam na farko yayi a yankin.

Bam na uku ya fashe ne kofar hedkwatar yan sanda na Kirkuk.

Yankin na Kirkuk dake dauke da dinbin yan sunni da shia tare ya tsira daga manyan hare haren bam na mota ba kamar Mosul da Baghdad ba,sai dai ana samun yan tsirarun fashewar bam na gefen hanya musamman ma a bangaren yammacin birnin na Kirkuk.