Ci gaban hare-hare a Irak
May 22, 2007Talla
Kussan mutane 40 su ka rasa rayuka, a ci gaba da yaƙe-yaƙen ƙasar Irak.
Hari mafi muni da yan ƙunar baƙin wake su ka kai a yau talata, ya rutsa da wata kasuwa, dake tsakiya birnin ɓagadaza, inda a nan take mutae 24 su ka kwanta dama.
Sauran hare-haren sun wakana a yakunan Diyala, da Adhamiyah.
Tashe-tashen hankula a ƙasar Irak, na ƙara ƙamari, duk da tsatsauran matakan tsaro ,da dakarun gwamnati da na Amurika su ka ɗauka, tun watan februaru da ya wuce.
A cikin wannan tsari, gwamnatin Irak tare da haɗin gwiwar Amurika, sun baza sojoji dubu 85 a birnin Bagadaza da kewaye.