1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban hare hare a Gaza

July 16, 2006
https://p.dw.com/p/BuqN

Israila ta fadada hare harenta a zirin Gaza,inda suka kashe Palasdinawa 4,daya a kudancin Gaza 3 kuma a arewacin yankin.

Wadannan hare hare a gaza kamar na Lebanon Isrialn ta kaddamar ne a kokarinta na karbo sojojinta 3 da yan gwagwarmaya sukayi garkuwa da su.

A yau din kuma dakarun yakin Israilan su sake kutsawa da tankunan yaki da karin jamian soji da jiragen yaki masu saukar angulu zuwa garin Beit Hanoun dake arewacin gaza,inda a cewarsu yan gwagwarmaya suke harba rokokinsu zuwa Israilan.

A kudancin gaza kuma wata mata ta rasa ranta a yayinda tankunan yakin Israilan suka harba albarusai kusa da inda gidanta yake.