1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da ziyarar shugaba HU na kasar Sin a Afrika

February 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuSk

A yau ne ake sa ran shugaban kasar China Hu Jintao,zai isa kasar Liberia kan ziyararsa zuwa wasu kasashen Afrika,karo na uku ke nan tun lokacinda ya karbi mulki a 2003.

Hu ya fara wannan ziyara ce daga kasar Kamaru inda yayi alkawarin baiwa kasar rance kudi fiye da euro miliyan 40.

Wannan ziyara ta HU ta nuna shaawar harkokin tattalin arziki da kasar Sin take da shi kann nahiyar Afrika,inda take bukatar albarkatun kasa da makamashi da nahiyar take da su wajen habaka tattalin arzikinta.

Sai dai kuma manufofin gwamnatin china game da Afrikan ya samu suka daga wasu bangarori saboda alaka da kasar ta Sin take dasu da gwamnatocin kasashe masu tsatsauran rayi kamar Sudan da Zimbabwe.