ci gaba da ziyarar Hu a afrika | Labarai | DW | 05.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ci gaba da ziyarar Hu a afrika

A yau shugaban kasar China Hu Jintao zai isa kara Namibia a ci gaba da rangadinsa zuwa wasu kasashen Afrika bayan alkawarin soke basusuka da saka jari na dala miliyan 800 da yayiwa kasar zambia.

HU da takawaransa na Zambia Levy Mwanawasa sun sanarda shirin kafa huldar ciniki da inganta tattalin arziki tsakaninsu.

Huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu ta karu da kusan kashi 12 a sheakarar data gabata da kusan dala miliyan 316.

Kasar ta China yanzu haka tana da kanfanoni kusan 180 a kasar ta Zambia.

Bayan Namibia shugaba Hu zai wuce zuwa kasashen Afrika ta kudu da Mozambique da Seychelles.