Ci-gaba da zanga-zangar yin tir da zanen cin mutuncin musulmi | Labarai | DW | 11.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci-gaba da zanga-zangar yin tir da zanen cin mutuncin musulmi

An sake gudanar da jerin zanga-zanga a kasashen musulmi don yin tir da zane-zanen batancin Annabi Mohammed SAW da wasu jaridu suka buga. Daruruwan masu zanga-zanga a Teheran babban birnin Iran sun yi arangama da jami´an tsaro a wajen ofishin jakadancin Faransa da ke wannan birni. Wasu masu zanga-zangar kuma sun yi ta jifar ofisoshin jakadancin Birtaniya da Denmark da duwatsu. An dai kame masu zanga-zanga da dama. An kuma gudanar da irin wannan zanga-zanga a Pakistan, India da kuma Malaysia. Rahotannin da suka iso mana na nuni da cewa jakadan Denmark a Syria ya bar wannan kasa saboda dalilai na tsaro. A Denmark aka fara buga zanen batanci kimanin watannin 4 da suka wuce, amma wasu kasashe sun sake bugawa. A yau al´umar musulmi a nan Jamus zasu gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da zane-zanen a gaban ofishin jakadancin Denmark dake birnin Berlin. An kuma shirya wani taron gangami a birnin Düsseldorf. A jiya juma´a dukkan jam´iyun siyasa a majalsar dokokin Jamus sun yi tir da tashe tashen hankulan da ake yi sannan a lokaci daya sun yi kira da a sasanta da duniyar musulmi.