1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da zanga zanga a kasashen musulmi na dunia

February 18, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7Y

Gwamnatin kasar Lybia, ta gurfanar da ministan cikin gida gaban kulliya, bayan tashe tashen hankullan da su ka gudana jiya, a birnin Benghazi, inda mutane fiye da 10, su ka rasa rayuka, a cikin arangama da jami´an tsaro, a yayin da su ke zanga zanga, gaban karamin opishin jikadancin Italia.

Al´umar kasar Lybia ta shirya wannan zanga zanga, domin tofin Allah tsine, ga Roberto Calderoni, ministan sake passalin dokokin Italia, wanda ya buga riguna dauke da zanen batancin nan, da wata jaridar Danmark, ta yi wa Manzan Allah, salla lahu Allaihi wa sallam.

Kungiyar Khadafi Fondation mai zaman kanta, a kasar Lybia, ta kiri gwamnatin Italia, ta dauki matakan hukunta wannan minister, muddun ta na bukatar al `ammura su daidaita.

A yammacin yau, ministan na kasar Italia, yayi murabus daga mukamin sa.

Praministan Italia, Silvio Berlusconi, ya yi hira ta wayar talho, da shugaban kasar Lyiba Muhhamad Khaddafi, a kan al´amarin.

A kasashe daban daban na dunia, musulmi na ci gaba da shirya zanga zanga.

A ranar yau assabar kimanin musulmi dubu 4 su ka hito, a biranen Duisburg da Kassel na nan Jamus, domin nuna Allah wadai ga zanen batancin, kazalika, irin wannan zanga zanga ta gudana a birnin London,na Engla,rahoton jami´an tsaron birnin ya bayana cewar a kalla musulmi dubu 10 su ka samu halarta.

A cen ma birnin Maiduguri na Tarayya Nigeria ,musulmi sun bukaci shirya irin wannan zanga zanga a ranar yau assabar amma suka ci karo da jami´an tsaro.