Ci gaba da yajin aikin sai baba ta gani a kasar Guinea | Labarai | DW | 18.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da yajin aikin sai baba ta gani a kasar Guinea

Shugabannin kwadago a kasar Guinea, sun ki shiga taron tattaunawar sulhu da bangaren gwamnati don kawo karshen yajin aikin sai baba ta gani da suka kira.

Kafafen yada labarai dai sun rawaito shugabannin kwadagon na cewa, zasu shiga taron sulhun ne kawai idan, shugaba Lansana Conte ya dage dokar sojin ta baci ne daya kafa a kasar.

Kwanaki 8 da fara wannan yajin aiki, mutane sama da dari ne suka rasa rayukan su,sakamakon ayyukan sojin kasar kann masu zanga zanga.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil adama suka soki lamirin sojin da musgunawa fararen hula, ta hanyar fakewa da dokar ta baci da aka kafa.