Ci gaba da tantana rikicin kasar Cote D`Ivoire | Labarai | DW | 31.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da tantana rikicin kasar Cote D`Ivoire

Nan gaba a yau ne za wata ganawa ta mussamman tsakanin Praministan rikwan kwarya na Cote D´Ivoire Charles Konnan Banny, da tawagar shugaban Afrika ta kudu Tabon Mbeki, da ke shiga tsakani a rikicin da ya ki ci, ya ki ceyewa a kasar Cote D´Ivoire.

Wannan haduwa ta biwo bayan wata makamanciyar ta, da a ka yi ranar asabar a birnin Pretoria tsakanin Konnan Banny da Tabon Mbeki da kuma waklilin Majalisar DinkinDunia Antonio Guteres.

Mahiman batutuwan da za a tantana sun hada da na hukumar zabe mai zaman kanta, da tsare tsaren baki daya.

Praminista Charles Konnan Banny, ya yi alkawarin shirya zaben gama gari a Cote D´Ivoire , cikin wa´adin da a ka tanada, wato a watan oktober na wannan shekara.

Saidai ya zuwa yanzu masu kula da harakokin da ke gudana a kasar, na nuni da cewa, abin na da kamar wuya, idan aka yi la´akari, da karin sabanin ra´ayoyi tsakanin bangarori daban-daban, masu gaba da juna a wannan kasa.