1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da musayar wuta a Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 13, 2014

Jaririyar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin mahukuntan Ukraine da 'yan awaren gabashin kasar ta rushe.

https://p.dw.com/p/1DBoU
Hoto: AFP/Getty Images/F. Leong

Mahukuntan kasar Ukraine, sun zargi Moscow da ruguza jaririyar yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma tsakaninsu da 'yan awaren gabashin kasar. Firaministan Ukraine din Arseny Yatseniuk ya ce shiga cikin kungiyar tsaro ta NATO ne kawai zai baiwa kasarsa damar kare kanta da abun da ya kira da shirin tarwatsata da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ke yi. Rahotanni sun bayyana cewa an samu musayar wuta a kusa da filin sauka da tashin jiragen sama dake gabashin Ukraine din a wani abu da ke zaman kama hanyar rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta da ta wanzu na tsahon kwanaki takwas tsakanin mahukunta Kiev da kuma 'yan awaren gabashin kasar masu goyon bayan Rasha. Su dai mahukuntan Moscow sun dage kan cewar basu da hannu cikin rikicin Ukraine din da yake kara kamari a kullum.