Ci gaba da kai hari a Niger Delta | Labarai | DW | 28.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da kai hari a Niger Delta

Kungiyar Niger Delta Avengers ta ce mayakanta sun kai hari kan bututun mai guda uku mallakar kamfanin Agip da Shell a garin Nembe da ke yankin mai arzikin man fetur a Najeriya.

Kungiyar ta bayyana kai wadannan sababbin hare-hare ne a shafinta na Tweeter, inda ta ce mayakanta sun kaddamar da harin ne da sanyin safiyar Asabar 28 ga watan nan na Maris da muke. Wani daga cikin mahukuntan jihar Bayelsa mai suna Bello Bina ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun ji karar harbe-harbe a yayin harin. Wannan dai shi ne karo na uku a jere da kungiyar ta Niger Delta Avengers take fasa bututun mai a yankin na Neger Delta da ke da arzikin mai a Najeriya. A watan Febarairun da ya gabata ne dai kungiyar ta bayyana, tare da fara kaddamar da hare-hare a bisa ikrarin neman 'yancin cin gashin kai a wannan yanki na Neger Delta.