Ci gaba da hari a Afghanistan | Labarai | DW | 15.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da hari a Afghanistan

A kasar Afghanistan fararen hula da dama sun rasa rayukansu bayan wata mota maƙare da bama bamai ta tashi a wajen ofishin gwamnan Kabul da kuma hedkwatar yan sanda ta birnin. Ƙungiyar Taliban ta ɗauki alhakin kai wannan hari,tana mai baiyana cewa ta yi niyyar kai harin ne kan yan sandan birnin Kabul. A dai ranar 5 ga watan Disamba ne wasu yan ƙunar baƙin wake na Taliban suka kara motar da suke ciki dauke da bama bamai kann motar sojojin Afghanistan inda aƙalla mutane 13 suka rasa rayukansu.