Ci gaba da binciken jirgin Egypt Air | Labarai | DW | 19.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da binciken jirgin Egypt Air

Wani jirgin sama na sojojin Masar ya gano wasu tarkace a gabar ruwan tsibirin Crete na kasar Girka a ci gaba da laluben jirgin saman Egypt Air mallakar kasar Masar da ya bace.

Wani jirgin sama na sojin kasar Masar ya gano wasu tarkace guda biyu a gabar ruwan tsibirin Crete na kasar Girka wadanda ake kyautata zaton na jirgin Egypt Air mallakar kasar Masar ne wanda ya fadi a tekun Baha Rum a cikin daren Laraba 18 ga wannan wata na Mayu da muke ciki dauke da mutane 66 da suka hdar da fasinjoji da kuma ma'aikatan jirgin. Kakakin rundunar sojan kasar ta Girka Vassilis Beletsiotis ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa suna shirin tura wasu jiragen ruwa zuwa wurin da jirgin saman ya tsinkayo wadannan tarkace domin a kwaso tare kuma da tantance su. Gidan talabijin na kasar ta Girka ERT1, ya sanar da cewa an tsinkayo tarkacen ne a wani wuri mai nisan mil 130 a gabar tsibirin Karpathos na kasar ta Girka. Rahotanni sun nunar da cewa fasinjojin da ke cikin jirgin saman na kamfanin Egypt Air wanda ya taso daga birnin Paris na Faransa a kan hanyarasa ta zuwa birnin Alkahira na kasar Masar sun hadar da 'yan kasar Faransa 15 da kuma 'yan kasar ta Masar 30.