Ci gaba da binciken hare haren bam a Nijeriya | Labarai | DW | 05.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da binciken hare haren bam a Nijeriya

Hukumomin tsaro a Nijeriya sun tsare darektan yakin neman zaben tsohon shugaban kasar, Janar Babangida bisa zargin fashewar bama bamai a kasar

default

Hukumar 'yan sandan ciki a Nijeriya ta tsare wani na - hannun daman tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya Janar Ibrahim Babangida - a jiya Litinin, bisa abubuwan da suka shafi tagwayen bama baman da suka tarwatse a Abuja, babban birnin kasar lokacin bukukuwan cika shekaru 50 da samun 'yancin kasar. Tsarewar da jam'ian hukumar leken asirin suka yiwa Raymond Dokpesi, babban darektan yakin neman zaben tsohon shugaban kasar Ibrahim Babangida ta sake za'fafa yanayin sha'anin siyasar kasar, a dai dai lokacin da kasar ke shirye shiryen tinkarar zabukan shekara ta 2011 - idan Allah ya kaimu.

Kungiyar 'yantar da al'ummar yankin Neija Delta ta MEND, yankin da kuma shugaban kasar Goodkuck Jonathan ya fito ne dai ta dauki alhakin kaddamar da hare haren na ranar Jumma'a, amma wasu rahotanni sun ruwaito shugaban kasar yana cewa wata kungiyar ketare ce ta kai hare - haren, kuma ya sha alwashin cafke wadanda ke da hannu cikin matsalar.

Tawagar yakin neman zaben Babangida ta bayyana cewar, Raymond Dokpesi ya mutunta gayyatar da hukumar leken asirin ta yi masa, amma ta ce tun a lokacin ne kuma aka hana shi ganawa da Lauyoyin sa, ga shi kuma a cewar tawagar ba'a bayyana wani dalilin gayyatarsa ba. Hukumomin tsaro a Nijeriya sun sanar da cafke mutane tara bisa zargin suna da alaka da wani jagorar kungiyar ta MEND Henry Okar, wanda a yanzu haka ke fuskantar shari'a a kasar Afirka Ta Kudu, inda ya ke yin gudun hijra bisa hare haren na ranar Jumma'a.

Wannan tsarewar ta zo ne a dai dai lokacin da shugaban na Nijeriya ya sanar da nadin wani dan kabilarsa ta Ijaw, kana tsohon hafsan tsaron Nijeriya Andrew Azazi a matsayin babban mai bashi shawara akan lamuran tsaro. Azazi dai zai maye gurbin Aliyu Gusau ne a mukamin, wanda ya ajiye aikin sa a watan jiya domin kalubalantar takarar Jonathan a zabukan kasar da ke tafe.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu