1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da bayyana sakamakon zaɓe a Siera Lenoe

August 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuDu

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a ƙasar Sierra Leone, ta bayyana kashi 45 cikin100, na yawan ƙuri´un da a ka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki, wanda da su ka wakana ranar asabar da ta wuce.

Ya zuwa yanzu, jam´iyar adawa ta APC ke kan gaba, a yayin da jam´iyar SLPP mai riƙe da ragamar mulki ke bi mata.

Ta la´akari da sakamakon da hukumar ta bayyana, ya zuwa yanzu, babu ɗan takara da zai yi nasara a zagaye na farko.

A game da haka,ya zama cilas a shirya zagaye na 2 ,a tsukin sati 2, bayan bayyana sakamakon ƙarshe na wannan zaɓe.

Tuni masu lura da al´amuran siyasa a ƙasar, na hasashen cewar, ɗan takara jam´iyar adawa ta APC, Ernest Koroma zai lashe zagaye na 2, a dalili da kyaukyawar mu´amilar sa da ɗan takara da ya zuwa yanzu ya zo sahu na 3.

A ɓangaren zaɓen yan majalisun dokoki, tunni jam´iyar APC mai adawa ta yi iƙirarin samun nasara, to saidai har yanzu ba a san ma cituwo ba, sai miya ta ƙare, inji hukumar zaɓen Siera Leone.