1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da ɓarin wuta a Somalia

April 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuMr

Bayan lafawar ƙura a daren jiya , yau da sahe birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia ya wayi gari cikin gurnanin rokoki, da amen wuta, a cigaba da bata -kashi tsakanin dakarun gwamnati, masu goyan bayan Ethiopia, da yan yaƙin sunƙuru na kotunan Islama.

A yau ne aka shiga sati na 2, a na kece reni, ba dare ba rana, tsakanin ɓangrorin 2.

Ya zuwa yanzu, mutane kussan 300 su ka rasa rayuka, a sakamakon wannan arangama, sannan dubunnai su ka shiga gudun hijira.

Dakarun gwamnati da na yan tawaye, sun yi kunen uwar shegu, a game da tayin Majalisar Ɗinkin Dunia, na tsagaita wuta.

ƙungiyoyin bada agaji, sun jaddada kira zuwa ga ɓangarorin 2,tare da cewar, su dubi girman Allah, su basu damar kai taimakon magani da abinci, ga yan gudun hijira, wanda ke cikin matsananciyar buƙata.