1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci da gumin 'yan ci rani a kan iyakokin Austriya da Hungary

Muhammad Nasiru AwalSeptember 16, 2015

Dubban 'yan gudun hijira ne suka tsallaka kan iyakar Nickelsdorf zuwa Austriya.Kana an soma yin rejistan 'yan gudun hijirar a kan iyakar Austriya da Hungary.

https://p.dw.com/p/1GXOj
Ungarn Österreich Grenze bei Nickelsdorf Polizisten
Hoto: picture-alliance/epa/H. P. Oczeret

Ƙasar Hungary ce ta yi jigilar 'yan gudun hijirar da jiragen ƙasa zuwa kan iyakar sannan a lokaci ɗaya ta rufe kan iyakarta da ƙasar Sabiya. Sai dai ba a rufe gaba-ɗayan iyakar tsakanin Sabiya da Hungary ba, inji wani mai suna Ali daga ƙasar Iraƙi, wanda ya ce ya biya wani ɗan sandar tsaron kan iyakar Hungary Euro 300, ya buɗe masa hanya. Sannan masu fataucin ɗan Adam na karɓar kowane mutum daya Euro 1500 don shiga da su Austriya.

Sansanonnin yin rejista 'yan ci ranin a kan iyakar Autriya

Nan dai ɗaya ne daga cikin sansanonin da aka kakkafa a ɓangaren Austriya na kan iyakarta da Hungary inda ake rajistar 'yan gudun hijira. Wasu daga cikin 'yan gudun hijira suna taimaka wa 'yan uwansu, ciki kuwa har da Ali daga ƙasar Iraƙi suna tattara shara. Wani mai fataucin ɗan Adam ya yi jigilarsu daga iyakar Sabiya da Hungary har zuwa cikin ƙasar Austriya.Ya ce "An ɗauke mu da wata ƙaramar motar safa wadda ta kai mu har kan iyaka. Mutumin da ya yi mana rakiya ya karɓe kowanenmu Euro 1500."Ali mai shekaru 27 ya yi wa Amirkawa aikin tafinta a Iraƙi, ana zarginsa da zama ɗan leƙen asiri, saboda haka bai samu aiki ba. Ya bi hanyar yammacin yankin Balkan zuwa kan iyaka tsakanin Sabiya da Hungary. Ya ce kuɗin da ya riƙa biya shi ne ya buɗe masa waɗannan kofofi.

Flüchtlinge Ungarn Serbien
Hoto: Alex Martin

Ana ci da gumin 'yan gudun hijira a kan iyakarkar Nickelsdorf

Su ma direbobi tasi kakarsu ta yanka saka a kan iyakar ta Nickelsdorf. Suna dai ci da gumin 'yan gudun hijirar, inda yanzu haka gaban cibiyar yi wa 'yan gudun hijirar rajistar, ya zama wata tashar motocin haya. Anton Buric ɗan aikin sa kai ne na ƙungiyar agaji ta Red Cross ya yi ƙarin haske:Ya ce: "Na samu labarin cewar direbobin tasin na karɓar kowane fasinja har Euro 350 a tafiya daga Nickesldorf zuwa birnin Vienna. A gani na wannan wani nau'in fataucin ɗan Adam ne."

Ungarisch-serbische Grenze in Röszke ist geschlossen
Hoto: DW/N. Rujević

Rahin tabbas a kan makomar 'yan gudun hijirar

Akwai rashin tsabta a manyan tantuna. Wasu 'yan gudun hijirar suna hutawa wasu na cajin wayoyinsu na salula. 'Yan agaji kuma na raba wa waɗanda suka tagaiyara burodi da tufafi. Yanzu haka dai yawan 'yan gudun hijirar da ke zuwa ya ragu idan aka kwatanta da 'yan kwanaki da suka wuce inji wannan matar:Ta ce: "Yanzu ba kamar a kwanakin baya ba lokacin da abubuwa suka yi muni. Sai dai komai na iya canzawa cikin ƙiftawa da bismilla.''

Flüchtlige nach ihrer Ankunft in Österreich
Hoto: picture-alliance/dpa

Hungary ta yi jigila dubban 'yan gudun hijira zuwa kan iyakar, kuma ba a san yawan waɗanda za su biyo baya ba. Kana musayar bayanai tsakanin Hungary da Austriya ba ta tafiya yadda yakamata.Yanzzu haka dai Ali na son sanin yaushe jiragen ƙasa za su fara tashi daga Vienna zuwa Jamus.