1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Christina Kirchner ta lashe zaɓen shugaban ƙasar Argentina

Mohammad Nasiru AwalOctober 29, 2007

Wannan dai shi ne karon farko a tarihin ƙasar ta Argentina da aka zaɓi mace a muƙamin shugabar ƙasa.

https://p.dw.com/p/C14q
Christina Fernandez
Christina FernandezHoto: AP

A lokacin da ta hau kan wani dandamali a otel din Interamericana, sa´o´i 3 bayan an rufe tashoshin zabe, magoya bayan Christina Kirchner sun barke da murna da sowa. Da farko ta yi kira da hadin kan al´umar kasar.

2. O-Ton Kirchner:

“Mun yi nasara da gagarumin rinjaye watakila mafi yawa tun bayan girke demukiradiya a kasar nan. Haka baya nufin an nuna mana wata gata ce a´a a daura da haka babban nauyi aka dora mana musamman bisa la´akari da wannan amincewa da al´umar Argentina suka yi mana.”

Bayan kai ruwa rana da aka yi ta yi da ´yan adawa a lokacin yakin neman zabe akan zargin cin hanci da kuma yin katsalandar a binciken hauhaar farashin kaya, yanzu Christina na kokarin gabatar da kanta a matsayin shugabar al´umar Argentina gaba daya. Baya ga haka ta nuna wani nauyi na musamman dake kanta a dangane da harkokin da suka shafi mata.

2. O-Ton Christina:

“Ina kira ga ´yan´uwana mata. Na san cewa akwai babban nauyi da ya kamata mu sauke. A matsayin mu na mata zamu iya ba da gudunmawa a fannoni da dama na fasalta iyali da ma tsarin siyasar duniya baki daya, wannan kuwa shi ne mafi muhimmanci.”

A cikin jawabin ta na tsawon mintuna 10 Kirchner mai shekaru 54 ta yi ta ba da misali da nasarorin da mijinta kuma shugaban kasa mai ci a yanzu wato Nestor Kirchner ya samu. A ranar 5 ga watan desamba zai sauka daga wannan mukami.

3. O-Ton Kirchner:

“Muna godiya da gagarumin aikin da gwamnatin shugaba Kirchner ta yi. Sahihan matakai da ya dauka da kuma watakila kurakuran da ya tabka sun nunar a fili yadda ya ke kaunar kasarsa. Mun gode kwarai kwarai da gaske.”

Yawan kuri´u na sama da kashi 40 cikin 100 da ta samu Chritina Kirchner ta yiwa babbar mai kalubalantarta kuma ´yar takarar jam´iyar kawance ta Coalition Civica, Elisa Carrio kintinkau. Sauran maza ´yan takara 12 ko kadan ba su kai labari ba. Idan aka hada yawan kuri´un da Christina da kuma Elisa suka samu to za´a ga cewa wannan shine karon farko a taerihin Argentina da mata suka samu kashi 2 cikin 3 na kuri´un da aka kada a wani zabe. Graciela Römer masaniya a alámuran zabe ta yi bayani tana mai cewa.

4. O-Ton Römer:

“Matan sun taka rawar gani ba wai don sun nesanta kansu daga tsoffin jam´iyun ba a´a ana daukarsu a matsayin mafiya iya rikon amana fiye da tsofaffin ´yan siyasa.”