1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Christian Wulff sabon shugaban Jamus

July 1, 2010

Majalisar taraiya ta zabi Christian Wulff ya zama sabon shugaban kasar Jamus

https://p.dw.com/p/O7Ym
Sabon shugaban Jamus, Christian Wulff gaban majalisar dokokin taraiyaHoto: dpa

Taron wakilan majalisar taraiya da wakilan jihohi 16 na Jamus ya zaɓi Cristian Wulff domin zama sabon shugaban ƙasar Jamus, bayan da ya samu ƙuri'u 625 a zagaye na ukku na zaɓen. Saleh Umar Saleh ya dubi tarihin sabon shugaban na Jamus wanda ya gaza samun rinjaye a zagaye na farko dana biyu na zaɓen.

Christian Wulff, mai shekarun haihuwa kimanin 50 da 'yan kai, ƙwararren lauya ne, dake jagorancin jihar Lower Saxony na ƙasar Jamus a matsayin pirimiya, tun cikin shekara ta 2003, wanda a yanzu kuma zai shugabanci Jamus bayan murabus na ba zatan da tsohon shugaban ƙasar Horst Köhler ya yi, abinda kuma zai sa ya kasance shugaban Jamus na farko – mafi ƙarancin shekaru.

Wulff, wanda ake damawa da shi a cikin harkokin jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tun yana da shekaru 20 a duniya, yana ɗan shekaru 34 ne kachal ya fara ƙalubalantar Gerhard Schroeder, wanda daga baya ya zama shugaban gwamnatin Jamus a yayin da shi Schroeder ke neman zama gwamnan jihar Lowaer Saxony.

Hakanan kuma, sau biyu yana fafatawa da shugaban babbar jam'iyyar adawar Jamus a yanzu ta Social Democrats Sigma Gabriel, gabannin ya yi nasarar ƙwace ikon jihar daga gareshi a shekara ta 2003. Ga dai abinda Cristian Wulff da kansa ke faɗi game da sha'anin siyasa.

" A tunani na abu ne mai kyau, ba wai kawai fagen siyasa ya kasance wuri na masu fada aji ba, amma har da samun banbancin ra'ayi a wannan fage. Nayi imanin cewar nan gaba za'a samu sassaucin ra'ayi da zaman lafiya, watakila kuma ana iya amfani da wannan a harkokin siyasa domin yin tasiri. A kwai lokuta da dama da zaa tinkari batutuwa ta fannoni daban-daban."

Ana ɗaukar Christian Wulff a matsayin mai matsaƙaicin ra'ayin riƙau, abinda ma yasa ake ganin shi ne dalilin daya sa ya kasance pirimiyan jihar sa ta Lower Saxony daya naɗa mace ta farko 'yar asalin ƙasar Turkiyya, kana musulma Aygul Ozkan domin ta zama minista a jihar. Wata 'yar siyasa anan Jamus ta kwatanta yadda take ɗaukar Gwamnan na Lower Saxony:

" Mutum ne mai tausayi, mai ƙwazo kuma ƙwararre."

Ɗabi'un da yake dasu na natsuwa da bin komai sannu a hankali, sun sa ya zama ɗaya daga cikin 'yan siyasar da suka fi farin jini anan Jamus. Wulff yama ci gaba da riƙe matsayin sa a cikin jam'iyyar CDU, wadda galibi ta mabiya ɗariƙar Katolika ce bayan sanarwar sakin matarsa da yayi wadda suka shafe tsawon shekaru 18 suna tare kana suke da 'ya mace guda. Daga baya kuma ya auro wata tsohuwar 'yar Jarida, wadda ya girme ta da shekaru 15 a cikin shekara ta 2008. A yanzunnan da ake magana kuma ta haifa masa ɗa namiji.

Wulff ya ce babban abinda ya bashi ƙwarin gwiwar neman shugabancin Jamus shi ne irin goyon bayan da yake da ita tun daga tushe:

" Mun samu ƙwarin gwiwa daga goyon bayan da muka samu daga jihar lower saxony, na yin amannar cewar suna hannu mai kyau, tare da la'akari da ayyukan da gwamnati ta yi madaidaici, ta hanyar zartar da hukuncin da ya dace akan wannan batu."

Ko da shike muƙamin shugaban Jamus na jeka na yi kane, amma ana ganin ɗarewar muƙamin da Cristian Wulff zai yi za ta taimaka gaya wajen ƙarawa ƙawancen jam'iyyun CDU da FDP da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke jagoranta farin jini.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Umaru Aliyu