Cholera a Zimbabwe | Siyasa | DW | 05.12.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cholera a Zimbabwe


Gwamnatin ƙasar Zimbabwe ta ƙaddamar da abunda ta kira dokar taɓace ga cutar kolarea dake cigaba da bazuwa kamar wutar daji a dukan sassan ƙasar.

Rahoton da hukumomin kiwan lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya  suka gabatar ya gano cewar, ya zuwa yanzu, kimanin mutane 600 suka rasa rayuka a sakamakon kamuwa da cutar, wadda ta haɗu da ƙazamin talauci tare da yinwa da al´ummar ƙasar ke fama da su.

  Baki ɗaya, kusan mutane 13.000 aka tabbatar da sun kamu da cutar, fiye da rabi a Harare babban birnin ƙasar da kewayensa.

To saidai daili da rashin ɗaukar mataki cikin lokaci,sannu a hankali ta fara bazuwa zuwa ƙasashe maƙwabta.

A halin da ake ciki dai, ƙasashe masu hannu da shuni, sun fara bayyana bada tallafi, wanda a cewar Dr Mathew Mushawedu na babbar asibitin Harare zai taimaka  a samu rangwame:

Duk da cewar an makkara, wajen kawo wannan ɗauki, da babu gwanda ba daɗi, muddun ƙasashen duniya suka gaggauta, ana iya killace cutar.

A halin yanzu asibitocinmu sun cika sun batse, kuma bamu da issasun kayan aiki da magani, saboda haka ƙaddamar da dokar taɓacen da gwamnati tayi zai baiwa ƙasashen ƙetare damar kawo ɗauki cikin gaggawa.

Tuni ƙasashen Engla, France , da Amurika sun ware kuɗaɗe masu yawa domin kai taimako ga yankunan da annobar ta shafa ta hanyar ƙungiyoyin agaji.

Kazalika, Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, kamar su Oxfam da Red Cross, na aiki dare da rana, domin taka birki ga bazuwar cutar, tare da haɗin gwiwar malumam kiwan lafiya na cikingida, kamar yadda DR Mushawedu yayi bayani: Yanzu zamu iya ƙoƙarinmu, domin hana yaɗuwar cutar, ta hanyar samar da magungunna da ruwan sha masu tsafta da kuma faɗakar da jama´a a game da matakin riga kafi na hanna kamuwa da ita.


Ƙasar Afrika ta kudu da cutar ta fara ɓullar mata, ta aika tawaga a birnin Harare, domin gani da ido halin da jama´a ke ciki, sannan ta bada shawara shirya taro na mussaman da zai haɗa ƙasashen SADC, da zumar ɗaukar matakan tallafawa Zimbabwe, inda bayan Cholera jama´a suka fara mutuwa  a dalili da matsananciyar yinwa.

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condolisa Rice, da Firaministan Kenya Raila Odinga, sun zargi shugaba Robert Mugabe da jawo wannan masifa ga Zimbabwe a saboda haka, sun buƙaci ya sauka daga karagar mulki.

Ranar litinin mai zuwa Ƙungiyar Tarayya Turai, zata shirya zaman taro, inda zata tsuke takunkumin da ta sakawa Zimbabwe.