China za ta samar da tashar Nukiliya a Sudan | Labarai | DW | 24.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

China za ta samar da tashar Nukiliya a Sudan

Hukumomin birnin Khartoum na Sudan a yau sun bayyana cewar wani kamfanin kasar Sin ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar samar da tashar Nukiliya a kasar ta Sudan da ke zama irin sa na farko.

Kamfanin harkokin Nukiliyar Sin mai suna CNNC ya sanya hannu kan yarjejeniyar da ma'aikatar samar da hasken wutar lantarki ne a jiya litinin domin samar da tashar da zata taimakawa kasar wajen samun hasken wutar lantarki.

Yarjejeniyar ata cewar mai magana da yawun ma'aikatar lantarkin Mohammed Abdelrahim zata tallafawa kasar a nan gaba domin bunkasa harkokin samar da makamashi don amfanin al'ummar kasar.

Yanzu haka dai Sudan din tana da karfin mega watt dubu uku a yayin da ke matukar bukatar samun karin megawatts nan da shekaru masu zuwa.