China ta yi kira da a nuna halin ya kamata a rikicin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 27.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

China ta yi kira da a nuna halin ya kamata a rikicin nukiliyar Iran

Kwana guda gabanin cikar wa´adin da kwamitin sulhun MDD ya ba Iran na ta daina aikace aikacen samar da sinadarin uranium, kasar Sin wato China ta yi kira da a nuna halin ya kamata a wannan takaddama. Wani kakakin ma´aikatar harkokin wajen China dake birnin Beijing ya ce warware wannan rikici ta hanyar diplomasiya shi ne zabi mafi a´ala ga dukkan bangarorin da abin ya shafa. Kwamitin sulhu na MDD ya ba Iran wa´adin zuwa gobe juma´a wato 28 ga watan afrilu na ta dakatar da shirin ta na nukiliya. To sai dai Iran ta ce alambaram ba zata dakatar da wannan shiri ba tun da ta na yi don samar da makamashi ta hanyoyin lumana.