China ta yi kaka-gida a Afirka?
Kasashen Afirka na maraba da tallafi daga China. A Addis Ababa na kasar Habasha, Fasinjoji na dokin shiga sabon jirgin kasa mai amfani da hasken wutar lantarki da kasar China ta samar kuma direbobin China ke tukawa.
Sabon tsarin abin hawa na daukar fasinja a Habasha
Alama ce ta ci-gaban fasaha a Habasha wato Ethiopia. Jirgin kasa na farko mai amfani da hasken wutar lantarki a Kudu da Saharar Afirka ya fara aiki cikin watan Satumba na shekara ta 2015. Duk da yake har yanzu yana matakin tsare-tsare ne, shirin ya sanya mazauna Addis Ababa farin ciki inda suke ganin tamkar ba gaskiya bane.
Daukar nauyi daga China
An dauki tsahon shekaru biyar wajen shimfida layin dogon da ke amfani da hasken wutar lantarki. Aikin ya lakume kudi dalar Amirka miliyan 475 kwatankwacin miliyan 436 na kudin euro. Bankin Exim na China ne ya dauki nauyin biyan kaso 85 cikin 100 na kudin.
'Yan kasar China a mazaunin direba
Ba wai kawai daukar nauyin shimfida layin dogon China ta yi ba. Ta kuma samar da direbobin jiragen kasan. Ma'aikatan kasar Habasha wato Ethiopia suke da alhakin bayar da tsaro a ciki da kuma tashoshin jiragen kasan.
Bin dogon layi
Fasinjoji na sayen tikiti. Ana sayar da tikiti kan birr biyu zuwa shida na kudin Habasha, kwatankwacin santi 25 na kudin euro. Kamar yadda aka san motoci kirar Tasi da Bus-Bus na cika da fasinja, haka sabon jirgin kasan ke cika da fasinjoji.
Duk a kasar waje!
Bayan gwaje-gwaje na tsahon watanni, an fara daukar fasinja da jiragen kasan a ranar 29 ga watan Satumba na 2015. Dubban fasinjoji na son shiga. Masu yawon bude idanu sun bi layi suna dokin shiga jirgin kasa mai dinbin tarihi a Afirka.
Yawan jirage, yawan tashoshi
Akwai shirin fadada ayyukan jiragen kasan masu amfani da hasken wutar lantarki a baki dayan bangarori hudu da za su kai mutum tsakiyar birnin. Kawo yanzu dai layukan dogo biyu kawai aka kammala. An tsara cewa jiragen za su yi dakon fasinjoji 60,000 kullum.
Cunkoson fasinjoji
Yayin da jiragen suka fara aiki ya zama wani sabon abu ga fasinjoji masu yawa. Yanzu dokin ya ragu sai dai fasinjojin na ci gaba da nuna farin cikinsu dangane da rashin tsadar tikiti da kuma isa guraren da suke son zuwa cikin sauri, musamman duba da yadda birnin Addis Ababa ke da cunkoso. A farkon jirgin ko karshensa ne kawai ake iya samun wurin zama sakamakon yawan fasinjoji.
Tashoshin jirgin kasa na karkashin kasa
Jirgin kasan na yin mafi yawan tafiyarsa ne a kan layukan dogo da ba na karkashin kasa ba. Amma akwai wasu tashoshin a karkashin kasa misali wannan tashar ta Medelik II.
Matsaloli
Dayawa daga cikin tashoshin jiragen kasan basu da saukin zuwa ga nakasassu. Akwai tashoshin da ke da matattakala mai amfani da wutar lantarki, sai dai ba dukansu ne ke aiki ba. Hakan ya sa tsofaffi da nakasassu na shan wahala kafin su samu jiragen kasan. Daukewar hasken wutar lantarki ma na kawo matsala ga ayyukan jiragen kasan.
Kariya daga layukan dogo
Wasu fasinjoji su kan tsallaka layukan dogon ba tare da sun duba sosai ko akwai jirgi mai tahowa daga wani gefen ba. Suna tunkarara hadari, kasancewar jiragen na gudu fiye da yadda mutane da dama ke tunani. Wannan wani babban kalubale ne ga ma'aikatan jirgin kasan.