China ta haramta fitar da naurorin Nuclear zuwa ketare | Labarai | DW | 17.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

China ta haramta fitar da naurorin Nuclear zuwa ketare

Hukumomin kasar Sin sun sanar da daukan sabbin matakai na kare ficewa da naurorin nuclear daga cikin kasar zuwa ketare,kwanaki kalilan da cimma yarjejeniya kann shirin nuclearn koriya ta arewa.Prime minista Wen Jiabao ya rattaba hannu a dokar dake haramta amfani da naurorin nuclearn da fasahar kera makaman atom ,ba tare da cimma wata yarjejeniya ba.Bugu da kari wannan doka zata kuma haramta wa masu shigowa da dangoginsu dominv darajawa dokar kasa da kasa,sai dai idan har ya hukumar kula da nuclear ta mdd ta amince da hakan.Duk dacewa wannan doka bata ambaci koriya ta arewa kai tsaye ba,an zartar da ita ne bayan cimma yarjejeniya a birnin Beijing ranar talata,a inda Pyongyang ta amince da rufe cibiyar nuclearnta.