China Taƙi ƙara dajajar kuɗinta
March 14, 2010Talla
Gwamnatin ƙasar China ta yi watsi da matsin lambar
ƙasashen yamma na ta ƙara darajar kuɗin ƙasar wato
Yen. Da yake jawabi ga taron majalisar al'ummar ƙasar
ta China, firimiya Wen Jiabao ya musanta zargin da
Amirka da Tarayyar Turai suke yi na cewa, China ta ƙi
daga darajar kuɗin ta na Yen domin ta ci gaba da
samun haɓaka na kayan da take fitarwa. Tun da farko
Kimanin wakilai dubu uku dake hallatar taron
majalisar al'ummar ƙasar, suka amince da kasafin
kuɗin da shugaban ƙasar Wen Jibao ya gabatar mata.
Kasafin na shekara 2010 goma zai cika giɓin da aka
samu a sakamakon rikicin tattalin arziki da duniya da
shiga. Ƙasar ta China ta tsara yadda za ta ƙara yawan
kuɗin da take kashewa domin tallafawa koma bayan
da aka samu, ta fannin kayan da take fitarwa.
Shugaban Wen Jibao ya kuma yi alƙawarin zai ƙara
yawan kayan da kasar ta China ke sayowa daga waje,
kuma ya buƙaci sauran ƙasashen duniya su ma su yi
hakan. Manufar shugabannin Beijing dai shine asamu
haɓakar tattalin arziki da kashi takwas cikin ɗari. Mawallafi: Usman Shehu Usman Edita: Ahmad Tijjani Lawal