China ce akan gaba wajen zartar da hukunce-hukunce na kisa | Siyasa | DW | 05.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

China ce akan gaba wajen zartar da hukunce-hukunce na kisa

Rahoton kungiyar Amnesty ya ce kasar China ta fi kowace kasa a duniyar nan zartar da hukuncin kisa akan fursinoninta

A cikin rahoton nata kungiyar Amnesty ta ce kimanin mutane 3400 ne aka zartas musu da hukuncin kisa a shekarar da ta wuce ta 2004 kuma China ce akan gaba. Mai yiwuwa adadin ya fi haka, saboda saboda ba lalle ba ne kowace kasa ta gabatar da cikakkun bayanai a game da yawan mutanen da ta yanke musu hukuncin kisa. Wannan bayanin na mai yin nuni ne da cewar dalilan da kasashen Jamus da faransa suka bayar a game da kyautatuwar manufofin ‚yancin dan-Adam a kasar China idan an kwatanta da shekara ta 1989 ya zama tamkar ba’a. Wani abin lura a nan shi ne kasancewar a taron hukumar hakkin dan-Adam da ake gudanarwa a birnin Geneva, kasar Amurka ba ta gabatar da wata shawarar kudurin dake Allah Waddai da kasar China ba, domin kuwa ita kanta Amurkan, kamar yadda bayanai na Amnesty suka nunar ba wani abin da ya banbanta ta da Chinar ko Iran da Vietnam. Dukkansu jirgi daya ne ke dauke da su a wannan manufa. Babban abin da ake zargin Chinar da shi shi ne rashin adalci a tsare-tsarenta na shari’a, inda galibi akan azabtar da fursuna har sai ya hakikance da laifin da ake zarginsa da aikatawa ala dole. Da kyar ne fursinonin ke samun wata kafa ta kare kansu. Bugu da kari kuma hukunce-hukuncen kisan ba kawai sun danganci miyagun laifuka ba ne, kazalika har da cinikin miyagun kwayoyi da almundahana da cin hanci. A misalin shekara daya da ta wuce an saurara daga dan majalisar wakilan China Chen Zhonglin yana mai batu a game da mutane kimanin dubu goma da akan zartar musu da hukuncin kisa a wannan kasa a kowace shekara. Kuma ko da yake yayi gyara ga wannan adadin da ya bayar, inda ya ce kiyasi ne kawai yayi, amma wannan mataki da ya dauka ya taimaka wajen gabatar da mahawara mai tsanani akan hukunce-hukuncen kisan a China. Wasu rahotanni na jaridun kasar sun fallasa kurakurai da dama na alkalai wajen yanke wa wasu fursinonin hukuncin kisa ba tare da sun aikata ainifin laifin da ake zarginsu da shi ba. A taron majalisar wakilai na bana an tsayar da shawarar gabatar da takardar duk wani hukunci na kisa da aka yanke a gaban kotun koli domin bita. Wannan manufar tana kunshe a daftarin tsarin mulkin China, amma an yi sama da shekaru 20 ba a aiki da ita. Su dai shuagabannin kasar, har kwanan gobe, suna tattare da imani ne cewar hukuncin kisan tamkar gargadi ne ga miyagun mutane, inda yawa-yawanci akan zartar da hukuncin a bainar jama’a domin zama darasi ga mutane. Amma fa har yau babu wani canjin da aka samu dangane da miyagun laifuka a kasar China. Mai yiwuwa da abu mafi a’ala shi ne a nemi hanyoyin cike gibin dake akwai tsakanin matalauta ‚yan rabbana ka wadata mu da masu hannu da shuni a wannan kasa mai bin tsarin kwaminisanci, a maimakon dukufa kacokam akan hukunce-hukuncen kisa tare da fatan al’amura zasu daidaita nan gaba.