1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Charles Taylor ya bayyana a kotun ƙasa da ƙasa

July 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuHE

A karo na farko, tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor, ya halaraci shari´ar da kotun ƙasa da ƙasa ke yi masa, a birnin The Hage, ko kuma la Haye dake ƙasar Hollande.

Tun ranar 4 ga watan da ya gabata, a ka fara wannan shari´a, amma tsofan shugaban ƙasar ya ƙi bayyana gaban kotu.

A na zarginCharles Taylor da leffika guda 11 da su ka hada da kissan gilla, fayɗe , handama da baba kere, da dai sauran miyagun leffika masu kama da haka.

A wani taƙaitacen jawabi da yayi gaba alƙalan,Charles Taylor, ya jaddada yin wasti da dukkan lefikan da a ke zargin sa da aikatawa.

Ɗan lokaci ƙalilan bayan fara wannan shari´a, kotu ta ɗage ta, har zuwa 20 ga wata mai kamawa.

Charles Taylor, shine shugaban Afrika na farko da ya taɓa gurfana gaban kotun ƙasa da ƙasa.