1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina a sahun kasashe masu bautar da dan Adam

Gazali Abdou Tasawa
June 28, 2017

Amirka ta saka kasar Chaina a jerin kasashen duniya masu yin fataucin dan Adam wannan kuwa duk da kusanci da gwamnatin Trump ta ke da a halin yanzu da takwararta ta Chainar. 

https://p.dw.com/p/2fWYD
Afghanistan ,oderne Sklaverei in Kabul
Hoto: DW/S.Tanha

Kasar Amirka ta sanya kasar Chaina a jerin kasashen duniya masu yin fataucin dan Adam kamar kasashen Siriya da Koriya ta Arewa wannan kuwa duk da kusanci da gwamnatin Trump ta ke da shi a halin yanzu da takwararta ta Chainar. 

A cikin wani rahoto kan fataucin dan Adam da ta wallafa a wannan Talata ma'aikatar harakokin wajen Amirkar, ta jera kasar ta Chaina a sahun kasashe 23 na duniya wadanda ba sa yin wani kokari wajen yaki da bautar da dan Adam kamar dai yadda sakataren harakokin wajen kasar ta Amirka Rex Tillerson ya yi karin bayani a lokacin gabatar da wannan rahoto: O-Ton Tillerson...

"Ya ce an jera Chaina a rukuni na uku a cikin rahoton musamman sabili da rashin daukar matakai na gaske wajen kawo karshen game bakin da ake yi da ita wajen bautar da dan Adam musamman mutanen da Koriya ta Arewa ke aikowa yi aikin karfi a Chaina"

Rahoton ya kuma saka Kasashen Afirka guda uku na Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da Kwango Brazzaville da Mali a jerin kasashen masu bautar da dan Adam, musamman dangane da abin da Amirkar ta kira sakaci da gwamnatocin wadannan kasashe ke yi wajen daukar matakan yaki da saka kananan yara aikin soja.