1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi: 'Yan adawa sun kira yajin aikin gama gari

Kiran da hadin gwiwar jam'iyyun adawa na kasar Chadi suka yi ga yajin aikin gama gari, bai yi wani tasiri ba a birnin NDjamena, inda ma'aikata suka fito domin karbar albashi a wannan rana.

Gwamnatin kasar ta Chadi dai da ke fama da matsalar tattalin arziki tun bayan faduwar farashin danyan mai a kasuwannin duniya, ta yi kira ga ma'aikatan da su je domin karbar albashin wata daya, abun da ya haifar da cinkoson jama'a a wannan safiya a gaban bankuna da duk wasu wuraren da ake biyan albashin ma'aikata. Kungiyoyin kwadago kasar ta Chadi suma dai sun kira wani yajin aiki ta sabili da rishin biyan su albashi. Da tsakiyar wannan ranar Talata da ke a matsayin ranar farko ta yajin aikin, zirga-zirgan ababen hawa ta gudana kaman yadda aka saba a cewar shaidun gani da ido, sai dai makarantun sun kasance a rufe, yayin da asibitoci ke yin takaitaccen aiki ta sabili da yajin aiki 'yan kwadago.