1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi ta zargi Sudan

Shugaban kasar Chadi Idriss Derby,a yau alhamis ya roki Kungiyar Taraiyar Afrika AU,da tayi Allah wadai da makwabciyarta Sudan saboda abinda ta kira goyon baya da gwamnati a Khartoum take baiwa yan tawayen da suke kokarin tunbuke shi daga mulki.

Idriss Derby ya zargi shugaba Omar al-Bashir na Sudan da kokarin tada zaune tsaye a yankin,inda ya ziyarci shugaba Olusegun Obasanjo na Najeriya domin kara baiyana zarginsa na cewa Sudan tana zama barazana ga kasarsa.

Chadin tace,gwamnatin Sudan ta shirya tare da bada umurnin kai hare hare har kashi biyu a garin Adre dake bakin iyakar kasashan biyu.