Chadi: Shugaba Idris Deby ya yi tazarce | Labarai | DW | 22.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi: Shugaba Idris Deby ya yi tazarce

Tuni dai wasu 'yan adawa a wannan kasa ta Chadi suka yi fatali da sakamakon zaben da suka bayyana da cewa an tafka magudi a cikinsa.

Shugaba Idris Deby na kasar Cadi ya yi nasara a zaben kasar da aka yi kamar yadda hukumar da ke tsara zabe a kasar ta bayyana cikin daren ranar Alhamis. Wannan dai zai ba wa Shugaba Deby dama ta dorawa da karin wasu shekaru 5 a kan karagar mulkin kasar bayan ya kwashe shekaru 26 ya na bisa karaga.

Tuni dai 'yan adawa a wannan kasa ta Cadi suka yi fatali da sakamakon zaben da suka bayyana da cewa an tafka magudi a cikinsa. Shugaba Deby dai ya yi wa abokin takararsa da ake ganin na rufa masa baya fintinkau a yawan kuri'u, inda ya samu sama da kashi 60 cikin 100 yayin da shi kuma Saleh Kebzabo ya samu kashi 12 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Sakamakon da Kebzabo ya ce babu komai cikinsa illa aringizo na kuri'u.

Sauti da bidiyo akan labarin