1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ba zata tilastawa ´yan gudin hijira Darfur komawa gida

April 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1f

Shugaba Idriss Deby na Chadi ya fadawa MDD cewa ba zai tilastawa ´yan gudun hijira kimanin dubu 200 daga lardin Darfur na yammacin Sudan da su fice daga sansanonin a Chadi ba. Hakan dai ta zo ne bayan da shugaban na Chadi ya yi barazanar korar ´yan gudun hijirar a cikin watan yuni idan gamaiyar kasa da kasa ta kasa warware rikicin lardin Darfur. Shugaban babbar hukumar MDD dake dake kula da ´yan gudun hijira ya ce shugaba Deby ya tabbatar masa da cewa ba zai tilastawa ´yan gudun hijirar komawa Darfur ba. Deby dai ya zargi Sudan da kokarin yin amfani da rikicin da ake yi a Darfur don haddasa rudami a yankin tsakiyar Afirka. Shugaban ya ce gwamnatin Sudan na marawa ´yan tawayen da suka kai hari a birnin N´djamena cikin makon da ya gabata baya, to amma gwamnati a birnin Khartoum ta musanta haka.