Ceton maáikatan haƙar maádanai a Afrika ta kudu | Labarai | DW | 04.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ceton maáikatan haƙar maádanai a Afrika ta kudu

A ƙasar Afrika ta kudu an sami ceto dubban maáikatan haƙar maádanai waɗanda suka maƙale a rami mai nisan fiye da kilomita biyu a ƙarƙashin ƙasa. Baá sami rahoton waɗanda suka jikata ba a haɗarin da rutsa da maáikatan a cibiyar hako maádanai ta Elandsrand dake kudu da yammacin Johannesburg a ranar laraba. Maíkatan haƙar maádanai kimanin 3,200 haɗarin ya rutsa da su. Ƙungiyar maíkatan ta ce wannan matashiya ce ga irin haɗarin dake tattare da aikin su wanda kuma ya kamata kamfanin yayi ƙoƙarin shawo kan lamarin. Kakakin kamfanin haƙar maádanan na Harmony Gold, Amelia Soares ta ce waɗanda aka sami kuɓutowa daga ƙarƙashin ƙasar suna cikin ƙoshin lafiya.