1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ceto Irland daga matsala tattalin arziki

Sadissou YahouzaNovember 16, 2010

Ministocin kudin kasashe masu amfani da Euro sun kuduri aniyar taimakawa Irland ta kubuta daga kariyar tattalin arziki

https://p.dw.com/p/QA6h
Ceton Irlandadaga fadawa matsala kariyar tattalin arzikiHoto: picture-alliance/dpa

Nan gaba a yau ne ministocin kudi na kasashe 16, da ke amfani da takaradar kudin bai daya ta Euro ,za su shirya zaman taro a birnin Brussels cibiyar kungiyar Tarayya Turai domin tattanawa, game da matsalar bashin da ya kai wa kasar Irland iya wuya.

Ya zuwa wannan lokaci dai Firayim ministan Irland, ya ce babu wata tattanawa da ta hada EU da kasarsa game da wannan matsala. A taron na yau, ana sa ran ministocin 16, su bullo da tsarin ceto kasar Irland tamkar yadda ta faru ga kasar Girka.

Kasar Irland dai na daya daga kasashen Turai, wanda su ka fi dandana radadin kariyar tattalin arzikin da ta rutsa da duniya shekaru biyun da su ka gabata.

Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu