1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

CENI ta sanar da ranakun zabe a Nijar

A Jamhuriyar Nijer hukumar zaben kasar mai zaman kanta CENI ta ce za ta gudanar da zabukan kananan hukumomi da na jihohi a ranar takwas ga watan Janairun shekara mai zuwa ta 2017.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijar CENI Ibrahim Boubé

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijar CENI Ibrahim Boubé

Bayan dage ranakun zaben fiye da sau biyu da hukumomin kasar suka yi, a yanzu kimanin 'yan takarar kansiloli a kananan hukumomi sama da 4000 ne za su fafata a yayin zabubbukan da kuma karin wasu daruruwan 'yan majalisun jihohi da ke zama zakaran gwajin dafi ga jaririyar demukradiyyar kasar. A yayin wani zaman taron majalisar hukumar zaben ta CENI da ya samu halartar wasu 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula ne dai, daukacin bangarorin suka aminta da sabon jadawalin wanda hukumar zaben kasar ta ce shi ne jadawalin karshe da take sa ran amfani da shi domin shirya zabubbukan. Jadawalin dai ya canji wani makamancinsa da hukumar ta shigar kuma aka yi masa kwaskwariya har sau biyu, abin kuma da ya janyo aka kara wa'adin magadan gari da 'yan majalisun jihohi da watanni shida.

Za a gudanar da zabukan kananan hukumomi da jihohi a Nijar

Za a gudanar da zabukan kananan hukumomi da jihohi a Nijar

Tanade-tanaden jadawalin zabe

Sabon jadawalin dai ta hukumar ta amince da shi ya tanadi wa'adin kwanaki 75 ga 'yan takarar domin ajiye takardunsu na neman a tsayar dasu, wanda zai kawo karshe a ranar 24 ga watan Oktoban wannan shekarar, a yayin kuma da za a shafe tsawon kwanaki 10 ana gudanar da yakin neman zabe da za a fara daga ranar 29 ga watan Disamban wannan shekarar. Sai dai daukacin zabubbukan da suka gabata a baya sun sha suka daga bangarori daban daban na siyasa da ma 'yan takara, koda yake 'yan adawar sun ce a shirye suke wajen shiga zabukan. Tun a shekarun 2004 ne dai Jamhuriyar Nijer ta rungumi tsarin bai wa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu ta hanyar bai wa talakawan kasar damar zaben masu wakilcinsu a matakin jihohi da yankuna don samun nasarar tafiyar da mulki da cin ribarsa.

Sauti da bidiyo akan labarin