Cecekuce tsakanin Iran da Amirka kan shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 12.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cecekuce tsakanin Iran da Amirka kan shirin nukiliyar Iran

Shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad ya zargi Amirka da yin amfani da rikicin nukiliyar kasarsa don yada farfagandar kyamar gwamnatin Teheran. A lokacin da yake magana a ci-gaba da ziyarar da yake kaiwa Indonesia shugaban Ahmedi Nijad ya ce ba ya tsammanin za´a kaiwa kasarsa wani hari na soji. An dai jiyo wani kakakin ma´aikatar harkokin wajen Amirka na cewa har yanzu kasarsa na kan bakanta na kin yin wata tattaunawa kai tsaye da gwamnatin Iran mai bin tsarin shari´ar musulunci. To amma akwai hanyoyi da dama na tuntubar juna tsakanin kasashen biyu. A wata hira da DW ta yi da shi, mai bawa tsohon shugaban Iran Mohammed Khatami shawara, wato Mohammed Shariati ya ba da shawara cewa kamata yayi Iran ta dakatar da shirin na nukiliya na wani kayyadadden lokaci, har sai an warware wannan takaddama.