Cece-kuce tsakanin Jamus da Turkiya | Labarai | DW | 06.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cece-kuce tsakanin Jamus da Turkiya

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya zargi mahukuntan Jamus da yin mulki irin na 'yan Nazi.

Tsamin dangantaka tsakanin Turkiya da Jamus

Tsamin dangantaka tsakanin Turkiya da Jamus

Kalaman na Erdogan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da tsamin dangantaka ke kara yin kamari tsakanin kasashen biyu, sakamakon kin amince wa da wasu jihohin na Jamus suka yi da  gangamin yakin neman amince wa da yi wa kundin tsarin mulkin Turkiya kwaskwarima da ministan harkokin kasashen ketaren Turkiyan ya shirya gudanarwa a Jamus din. Ministocin na Turkiya dai sun shirya gudanar da gangami na neman al'ummar kasarsu mazauna Jamus su amince da yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarimar wanda hakan zai karawa Erdogan karfin iko da kuma yin watsi da ofishin firaminista, sai dai jihohin Jamus din da dama sun ki amince wa da a gudanar da gangamin bisa abin da suka bayyana da dalilai irin na tsaro. Erdogan wanda ya bayyana cewa matakan hana gangamin a Jamus ba shi da maraba da mulkin 'yan Nazi, a yayin wani gangami da matan kasar suka shirya a birnin Santanbul, ya yi takaitaccen bayani dangane da abin da ya shafi cin zarafin mata a kasarsa, wanda kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta bayyana cewa ya kai makura a Turkiyan. Wadannan kalamai na Erdogan dai sun fusata 'yan siyasar Jamus din inda har ma ministan shari'a Heiko Maas ya bayyana kalaman nasa da na neman tayar da zaune tsaye, yayin da mataimakiyar shugabar jam'iyyar CDU da ke mulki Julia Klöckner ta bukaci da lallai ya nemi afuwa.