Tawagar matukan jiragen ruwa na kungiyar Doctors Without Borders a gabar tekun Mediteranean na sanya idanu kan jiragen 'yan ci rani wadanda suka fuskanci matsala don kai musu dauki, sai dai har yanzu kungiyar ta ki amincewa ta saka hannu a kan wasu sharuddan da gwamnatin Italiya ta gicciya musu a kan aikin da suke yi a gabar ruwan tekun Bahar Rum