Cece-kuce kan alakar Trump da Rasha
May 17, 2017Jaridar New York Times ta Amirka ce dai fito da wannan sabon bincike, al'amarin da wasu 'yan majalisar Amirka ke cewa ya na da hadari ga gwamnati. Shi dai wannan binciken na zuwa ne a lokacin da shugaba Donald Trump ke fuskantar kalubale banyan sallamar tsohon shugaban hukumar binciken manyan laifukan kasar James Comey, bayanan da fadar White House ta yi saurin musantawa.
Jaridar New York Times dai ta ce a ranar 14 ga watan Fabrairun bana shugaba Trump ya gana da tsohon shugaban hukumar FBI James Comey dangane da alakar Michael Flynn da kasar Rasha kuma cikin bayanan da suka yi wadanda suke a rubuce shugaba Trump ya bukaci da a rufe wannan batun bayan sallamar tsohon jami'in da ya yi tun farko, bayanan da masu kallon lamura a kasar ke wa kallon kokarin kwancewa Trump zani a kasuwa ne a yanzu.
Bayanai dai sun tabbatar da cewa shugaba Trump ya sallami tsohon shugaban leken asirin soji Michael Flynn daga fadar White House ne kan alakarsa da Rasha, kwana guda kafin ganawarsa da James Comey da aka sallama. Sallamar Mr Flynn dai kai tsaye alamu ne na shakkun da mahukunta ke nunawa dangane da hadarinsa ga Amirkar da kutunguilar Rasha kamar yadda sashin shari'ar Amirka ke zargi.