1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece kuce game da yaki da cin hanci na Biya

Umaru AliyuJune 20, 2012

Majalisar dokokin kamaru na samun rarabuwa kawuna game da ci gaba da tsare wasu manyan jami'ai bisa zargin badakalar kudaden al'uma ciki har da Marafa Hamidou Yaya.

https://p.dw.com/p/15Ihg
Cameroon Incumbent President, Paul Biya , wave to his supporters after casting his vote during the Presidential election in Yaounde, Cameroon, Sunday, Oct. 9. 2011. Cameroonian go to the polls Sunday to elect a new President (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Hoto: AP

Ci gaba da tsare na hannun daman shugaba Paul Biya na Kamaru, ciki kuwa har da tsohon firaminista Chief Ephraim Inoni da kuma tsohon sakataren gwamnati Marafa Hamidou Yaya, na raba kawunan 'yan siyasan kasar. dukkaninsu biyu, ana zarginsu ne da laifin cin hanci da kuma sama da fadai da dukiyar kasa. Amma wasu daga cikin masu fada aji a majalisar dokokin kasar na ganin cewa wannan lamari bita da kulli ne kawai.Dan majalisa Joseph Banadzem, shi ne shugaban rukunin 'yan majalisa da aka zaba karkashin jam'iyar SDF mai adawa. Ya yi imanin cewa tsaresun da akayi yana da alaka da batun siyasa.

"Akwai manufoffi na siyasa masu karfi a wannan tsarewar da akayi dama yadda ake kulawa da Jami'an da abin ya shafa. Akwai manyan Jami'an da suka amince sunyi sama da fadi da kudade suka kuma wanke kansu: to ka gani akwai son kai kenan. Wannan a bayyane yake cewar batu na baya bayan nan shine na Marafa inda rikicin ya fara ne sanadiyyar baiyyana aniyarsa na tsayawa takarar shugaban kasar."

Präsidentschaftspalast Palais d'Etoudi Schlagworte: Kamerun, Yaoundé, Yaounde, Jaunde, Präsidentschaftspalast, Präsident, Wahl
Fadar shugaban kasar KamaruHoto: Dr. Dirke Köpp

Shi dai Marafa Hamidou Yaya, shine tsohon sakataren gwamnatin kasar ta kamaru, kana tsohon ministan cikin gida. Lokaci da ya ke rike da wannan mukami ne, shugaba Paul Biya ya yi ma kundin tsarin mulki kwaskwarima: lamarin da ya ba shi damar yin tazarce. Amma kuma wasu daga cikin yan majalisun Kamaru kamar Joseph Banadzem suna da yakinin cewa wasu mutane sun kafa wata kungiya mai lakabin G Eleven dan su fitar da dan takarar da zai maye gurbin shugaba Paul, saboda mayar da hankali akan cewa kudin jam'iyar CPDM mai mulki bai baiyana wanda zai gaji shugaban ba. Kazalika kundin tsarin mulkin kasar bai baiyyana shugaban ba a matsayin halarttacen dan takara ba. sannan kuma Biya yayi gum akan lamarin.

"Wadannan yan kungiya ta cikin gida mai suna G Eleven sun hade ne saboda ganin cewa za,a gudanar da zabe a shekara ta dubu biyu da goma sha daya kasancewar sun san shugaban ba zai sake yin takara ba. Sai kuma gashi kundin tsarin mulki yayi gyara ya kuma bashi damar sake tsayawa takarar wanda hakan yasa akai daidai dasu ta hanyar chapke wasu daga cikinsu wanda a yanzu haka suke tsare wasu kuma suka tsere."

Al'uma na ta bayyana ra'ayoyin da suka sha babban game da cafke tsaffin ministocin na kamaru. Sai dai kuma ministan watsa labaran kasar, kana kakakin gwamnati wato Issa Tchiroma Bakary ya je batun ba haka ya ce gwamnati a shirye ta ke ta tabbatar da gaskiyar lamarin.

Der kamerunische Minister für Kommunikation, Issa Bakary Tchiroma, und der stellvertretende Generalsekretär der Regierungspartei RDPC, Grégoire Owona Schlagworte: Kamerun, Minister, RDPC, Wahlen,
Ministan watsa labarai Issa Bakary TchiromaHoto: Dr. Dirke Köpp

"Ko kun san halin da ake ciki? Ana iya yi wa mutane karya. Kuma dole ne mu tgsaya mu ga mun gaya musu gaskiya. zaman lafiya ba abin da za'a zauna ana tababa a kai ba ne. Mun yarda za mu zama tsintsiya madaurinki daya don mu asassa zaman lafiya. A shirye mu ke mu dauki mataki don ganin cewa an tabbatar da zaman lafiya"

Ko shi ma shugaba Paul sai da ya baiyyanawa magoya bayansa lokacin babban taron jam'iyar CPDM mai mulki cewa babu gudu babu ja da baya ga aaniyarsa ta yaki da cin hanci da karbar rashawa.

Mawallafi: Aisha Ibrahim Abubakar
Edita: Mouhamadou Awal