Cece Kuce Akan Taron Duniya Na Larabawa Da Musulmi A Berlin | Siyasa | DW | 16.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cece Kuce Akan Taron Duniya Na Larabawa Da Musulmi A Berlin

Ministan cikin gida na Jamus Otto Schily ya ce zai yi bakin kokarinsa wajen hana wanzuwar wani taron Kasashen Larabawa da Musulmi da aka shirya gudanarwa a Berlin watan oktoba mai zuwa saboda a ganinsa makasudin taron shi ne kara yayata zazzafan ra'ayi na addini da kuma ba da goyan baya ga matakan ta'addanci.

Ministan cikin gida na Jamus Otto Schily

Ministan cikin gida na Jamus Otto Schily

A ‚yan kwanamkin da suka wuce ne aka samu bayani daga ma’aikatar cikin gida dake Berlin cewar, ma’aikatar na shirye-shiryen hana taron kasashen Larabawa da Musulmi na farko a nahiyar Turai, amma kakakin ma’aikatar ta cikin gida ya ki yayi bayani filla-filla, inda ya ce karamar hukumar Berlin ce ke da alhakin lamarin. Amma a yanzun sai ga shi an wayi gari shi kansa ministan cikin gida Otto Schily ya uwa-yayi-makarbiya a takaddamar, inda yake cewar:

Har abada ba zamu yarda birnin Berlin ya zama dandalin gudanar da wani taron dake da nufin nuna adawa da kyamar Yahudawa da Bani Isra’ila ba. Taron da makasudinsa shi ne yayata farfagandar ta’addanci a Isra’ila da Iraki, bisa ikirarin adawa da halin da ake ciki. Wannan ba abu ne mai karbuwa ba.

Bayanai dai sun nuna cewar taron an shirya gudanar da shi ne daga daya zuwa uku ga watan oktoba, amma ba a bayyana takamaiman wurin da za a gudanar da shi, tare da halarcin daruruwan wakilai daga dukkan sassa na duniya ba. Masu alhakin shirya taron, kamar yadda aka nunar, suna amfani da yanar gizo ta na’ura mai kwakwalwa domin gabatar da kiran daukar matakan adawa a Iraki da Palasdinu. Kazalika taron na da nufin kafa wata kungiyar adawa ta kasa-da-kasa. Amma Gabriel Daher daya daga cikin masu alhakin shirya taron yayi fatali da dukkan koraf da zargin yayata akidar ta’addanci da zazzafan ra’ayi na addini da ake yi inda ya kara da cewar:

Ba zamu yi wata rufa-rufa a game da matsayinmu ba na adawa da rashin adalci da kuma ba da cikakken goyan baya ga masu fama da radadin mamaye a yankunan da lamarin ya shafa.

To sai dai abin kaico shi ne yadda shafin na yanar gizo da masu alhakin shirya taron suka gabatar ke da nasaba da dakarun al’aksa na kungiyar Fatah ta malam yassir Arafat. A nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta fara nazarin yiwuwar hana wasu daga cikin wakilan dake da niyyar halartar taron bisar shigowa kasar. Ministan cikin gida Otto Schily ya ce gwamnati na da cikakken ikon kin ba da bisar, to sai dai da wuya a tabbatar cewar kowane matafiyi na da niyyar halartar taron. Wani abin mamaki kuma shi ne yadda aka soke ajiyar dakuna 150 da aka yi a wani otel dake Berlin, wanda aka ce a nan ne aka shirya yi wa mahalarta taron masauki. Kazalika babu wani bayani da aka samu a game da cewar an yi hayar wani zauren taro a yankin Berlin Neukölln, inda Musulmi ke da rinjaye a birnin na Berlin.