Cece-kuce a game da zargin tsegunta bayanan sirri. | Siyasa | DW | 28.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cece-kuce a game da zargin tsegunta bayanan sirri.

Gwamnatin Jamus ta karyata zargin cewa ta tseguntawa Amurka bayanan sirri domin karya lagon Saddam Hussaini alokacin yakin Iraqi.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeir

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeir

A makon da ya gabata, jaridar New York Times ta baiyana cewa wasu jamiái biyu na hukumar leƙen asiri ta kasar Jamus sun sami takardun bayanai na dabarun yaki da harkokin tsaro na tsohon shugaban ƙasar Iraqi Saddam Hussaini wanda ke baiyana yadda ya shirya tunkarar sojojin taron dangin da kuma bada cikakken tsaro ga birnin Bagadaza. Jaridar ta ce rawar da Jamus din ta taka yana kunshe ne a cikin wani kundi na dabarun sojin Amurka a lokacin yakin Iraqin . Da yake jawabi ga manema labarai, kakakin gwamnatin Jamus Ulrich Wilhelm yace gwamnatin ta yi mamaki matuka da rahoton wanda yace bashi da tushe balle makama. Yace zargin cewa jamián leken asirin Jamus sun tseguntawa Amurka bayanan sirri don karya lagon Saddam Hussaini ba gaskiya bane. Yace babu daya walau hukumar Leken asirin ta Jamus ko gwamnatin tarayyar Jamus da ya san wannan alámari ko kuma wata ganawa da ta wanzu tsakanin Saddam Hussaini da jamián leken asirin Jamus a ranar 18 ga watan Disambar shekara ta 2002 kamar yadda jaridar ta baiyana.

A nasa bangaren mai magana da yawun dakarun sojin hadin gwiwar karkashin jagorancin Amurka yace babu shakka sun gudanar da nazari a game da dabarun yakin amma babu inda suka baiyana cewa Jamus ce ta baiwa Amurka bayanan sirri a game da yakin na Iraqi. Shi kuwa kakakin Jamíyar SPD a kan manufofin cikin gida, Dieter Wiefelsputz ya yi kira ga jamaá da su kwantar da hankalin su a game da wannan cece-kuce da ake yi. Yace wannan ba shi ne karo na farko da jaridun Amurka ke gabatar da wasu rahotanni da kan tada hankalin jamaá a nan Jamus ba, kuma galibi a karshe sai a ga dukkan binciken da suka yi ba shi da wata madogara. Yace shi kan sa a yanzu alámura sun kai masa Iya wuya a game da yin sharhi a kan wadannan zantuttuka da ba su da amfani. Yace mu dai a nan Jamus muna iya kwantar da hankalin mu domin kuwa gwamnati da shugaban hukumar leken asirin kasar ta Jamus duka sun fito fili sun karyata wadannan rahotanni.

Idan dai baá manta ba gwamnatin da ta shude karkashin jagorancin Gehard Schröder ta ya sha fitowa fili ta yi kakkausar suka tare da nuna adawa da yakin da Amurka ta hjagoranta a Iraqi, ko da yake gwamnatin bata kuma boye takaitaccen taimakon da ta yiwa gwamnatin Amurka ba. Wadanann taimako kuwa sun hada da bada tsaro ga sansanonin Amurka dake nan Jamus da taimakawa sojojin dake karkashin kungiyar tsaro ta NATO.

Hukumar leken asiri ta kasar Jamus ta ce an mika cikakken bayanai ga majalisar dokoki domin gudanar da bincike a game da ayyukan da jamián biyu na leken asirin Jamus suka gudanar daga 15 ga watan Fabrairu shekara ta 2003 zuwa 2 ga watan Mayu shekara ta 2003 a yayin da suke kasar Iraqi. Biyu daga cikin jamíyun adawa sun baiyana cewa basu gamsu da binciken da aka gudanar ba, inda suke kira da a fadada bincike. Max Stadler dan majalisa daga jamíyar Liberal Free Democrat yace idan har bayanin da jaridar ta wallafa ya kasance gaskiya, to kuwa zai bude wani sabon babi a harkokin gudanarwar jamian tsaron.